January 22, 2025

Gwamnan Abba ya zargi gwamnatin Ganduje da cin hanci da rashawa da gazawa wajen tsara birane.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu.

Gwamnan jihar Kano da ke Najeriya Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da wasu muhimman sauye-sauye a harkokin tafiyar da filaye tare da sabunta tsarin kula da ma’aikar ƙasa ta jihar Kano (KANGIS) da kuma ɓangaren gudanarwa na ma’aikatar filaye da tsare-tsare.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya bayyana hakan a matsayin wani ci gaba na samar da ingantaccen tsarin kula da filaye.

Ya kuma ba da sanarwar sake ba da cikakkun takardun shaidar mallaka don tabbatar da sahihancin bayanan filaye, saka hannun jari, da warware taƙaddama, ya na mai kira ga masu mallakar filayen da su karɓi wannan tsarin cikin gaggawa.

“Su na ɓata wa kan su lokaci ne kawai, kwanan nan kotu to kori shi kansa Kwankwason daga NNPP saƙon Madaki ga masu son a tsige shi.

Ƴan majalisar wakilai na NNPP sun amince da tsige Ali Madaki a matsayin mataimakin shugaban marasa rinjaye.

Kano Pro-pa ta nemi Gwamnatin Kano ta tsayar da ginin wasu ajujuwan karatu.

Gwamnan ya kuma zargi gwamnatin da ta shude da cin hanci da rashawa da gazawa wajen tsara birane, in da ya sha alwashin maido da zaman lafiya ta hanyar yin garambawul don samar da cigaba Mai dorewa.

Gyare-gyaren dai sun hadar da tsarin tattara bayanai na zamani wato (GIS) inganta tsara birane, haɓaka haraji, da kuma kawo karshan ɓarnatar da kudaden shiga.

Matakan sun kuma hadar da hana rabon filayen da basu kamata ba da kuma kafa kwamitin kula da ci gaba na jiha don magance kalubalen ci gaban birane da kuma kare al’adun al’ummar Jihar Kano.

Daga bisani kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cikakkun gyare-gyaren da za’a gudanar a ma’aikatar wanda a yanzu aka samar da kayan aikin na zamani don bunkasata wanda hakan ke nuni da yadda gwamnatin ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da kuma samar da cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *