Daga Suleman Ibrahim Modibbo
A wani saƙo da ya wallafa a shafin na Facebook mai taken #ArewaMuFarka gwamnan jihar Bauchi da ke Arewacin Najeriya Sanata Bala Muhammad Abdulƙadir, ya buƙaci ƴan Arewacin ƙasar da su tashi su farka musamman malamai, iyaye da shugabanni.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu hotunan da bidiyon da yaran da rundunar Ƴansandan Najeriya ta gurfanar gaban kotu tarayya su ka fara yawo kafafen sada zumunta cikin wani yanayi na ban tausayi, in da ana tsaka da sauraron ƙarar yara huɗu daga cikin waɗanda ake zargin su ka yanke jiki su ka faɗi wasu na ihun cikin su, wasu kuma duk sun ƙeƙashe sun rame cikin yanayin nuna alamun yunwa, abin da ya sa dole alƙalin ta dakata da shari’ar domin a duba su.
An kama waɗanda ake zargin ne a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da aka gudanar a faɗin Najeriya tsakanin 1 zuwa 10 ga watan Agustan 2024.
Gwamna Bala, ya nuna alhini da kaɗuwar ganin halin da yaran ke ciki “na samu kaina cikin firgici da tashin hankali bayan kallon faifayin bidiyon yaran da aka gurfanar da su jiya a gaban kuliya bisa tuhumar yunƙurin kifar da gwamnati, sata da kuma tada-zaune-tsaye yayin zanga-zangar #EndBadGovernance watanni biyu suka shuɗe.”
“Halin tagayyara, matsananciyar yunwa da rashin abinci masu gina jiki da ke bayyane a jikin yaran, ya fallasa irin riƙon sakainar kashi da cin zarafin da ake yi wa al’umma a gidan gyaran hali ko hannun jami’an tsaro, uwa uba kuma ya tona ƙalubalen rashin nagartaccen shugabanci da magana da murya ɗaya da Arewa ke fama da su,” in ji Gwamnan.
Gidauniyar OVPCF Ta Tube Shugabanta Na Bauchi, Tare Da Sallamarsa Baki Ɗaya.
Gwamna Uba Sani Ya Amince Da Biyan Dubu 72 Mafi Ƙarancin Albashi A Kaduna.
Gwaman ya jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa “Yayin da na ke jajanta mana duka a matsayin mu na iyaye kuma shugabanni, ina kira da babbar murya ga hukumomin tsaro da sashen Shari’a da su martaba yancin faɗin albarkacin baki da kuma haƙƙin ɗan Adam, su kuma yi dubi da halin ƙunci da tsadar rayuwa da muke ciki su saki waɗannan yara.”
“Ta ina wanda bai iya ciyar da kansa abinci sau uku a rana ba zai iya biyan Naira miliyan goma a matsayin beli? A maimakon haka, ina kira da a sassauta tare da jan kunnen waɗanda aka tabbatar da hannun su cikin aika-aikar,” in shi.
A karshe ya kuma ƙara yin kira ga iyaye, malamai da shugabannin mu da su tashi su farka a Arewacin Najeriya.
An dai kama yaran da ake tsare da su ne a garuruwan Kano, da Katsina, da Gombe, da Abuja, da Jos, da Kaduna.