Gwamnan Gombe Ya Sa Hannu Kan Takardar Yarjejeniyar Samar Da Tashar Wutar Lantarki A Jihar.

Daga Abdul’aziz Abdullahi

Gwamnatin jihar Gombe ta kulla yarjejeniyar da wani shararren kamfani mai suna China18th Engineering, wanda zai samarwa jihar tashar wutar lantarki megawatt 100 mai amfani da hasken rana (Solar).

Gwamna Inuwa Yahaya, ya rattaba hannun kan takardar yarjejeniyar a gidan gwamnati da ke Gombe, in da ya bayyana muhimmancin samar da tashar wutar lantarkin ta fuskar bunkasa tattalin arziki da kuma magance matsalar wutar lantarki da ake yawan samu.

Gwamnan ya kuma yi tsokaci kan matsalar rashin wutar lantarki da aka samu a fadin kasar a baya-bayan nan da ya shafi Gombe da sauran sassan Arewacin Najeriya, in da ya jaddada cewa samar da tashoshin wutar lantarki mallakar jihohi za su iya dakile wannan matsala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Proudly powered by WordPress | Theme : News Elementor by BlazeThemes