September 22, 2021

Gwamnan Gombe ya yi jimamin rasuwar Manjo Danbabu, da matar sa, da ‘yar sa wadanda suka rasu sanadiyyar hatsarin mota

Page Visited: 168
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 6 Second

 

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya yace ya kadu matuka da jin labarin rasuwar Manjo Auwal Danbabu Muhammad, wadda ya rasu sanadiyyar hatsarin mota tare da Matar sa Fadila Auwalu Shehu Brema da kuma ‘yar su daya tilo Aisha. Hatsarin ya faru ne kan hanyar Zamfara zuwa Kano.

Kafin rasuwar sa, Manjo Auwal Danbabu jami’i ne a rundunar sojin Najeriya Birgediya ta 1 dake Gusau a Jihar Zamfara.

A jiya ne kuma Gwamnan ya jagoranci tawaga zuwa ta’aziyya wa iyalan Alhaji Shehu Brema a gidan su dake Kumbiya-Kumbiya, inda ya mika ta’aziyyar sa bisa wannan babban rashi.

Yace rasa dan uwa abu ne mai zafin wadda da wuya a mance shi, musamman irin mutuwar dake faruwa cikin ganiyar shekaru.

Yace “Mutuwar matashin dake kan ganiyar kuruciya abu ne dake karya zuciya ga kowa, musamman ma ga iyalai da ‘yan uwa da abokan aiki. Muna tare da ku cikin wannan hali na jimami, kuma a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe, muna mika ta’aziyyar mu tare da addu’ar Allah ya gafarta musu ya bamu hakurin jure rashin, ya kuma sa Aljannah Firdausi ta zame musu makoma.”

A yayin ziyarar ta’aziyyar, gwamnan ya samu rakiyar shugaban ma’aikata na gidan gwamnati, Alhaji Abubakar Inuwa Kari, da shugaban ma’aikata Alhaji Bappayo Yahaya, da kwamishinoni da mashawartan gwamna da sauran hadimai.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us