Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Gwamnan jihar Neja ya umurci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka gani da askin Dada - Martaba FM Gwamnan jihar Neja ya umurci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka gani da askin Dada - Martaba FM

A wani mataki mai tayar da kura da aka dauka don dakile karuwar rashin tsaro a jihar Neja, Gwamna Umar Bago ya umurci jami’an tsaro da su kama duk wanda aka gani da gashin askin Dada ko sanya weavon, ya na bayyana irin wadannan salon kwalliya a matsayin alamar rashin tarbiyya.

Umarnin wanda aka dauka cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, ya haifar da mahawara mai zafi a cikin al’umma da kungiyoyin fararen hula; Gwamna Bago yayin wata ganawa da jami’an tsaro, ya umurci a kama irin wadannan mutane, a aske musu gashi, sannan a ci su tara.

“Ba za mu yarda da rashin kunya ko kadan ba,” in ji gwamnan. “Duk wanda aka gani da dreadlock, a kama shi, a aske masa gashi kuma a ci shi tara. Idan aka samu wani da weavon, ayi masa kamar dan fashi da makami.”

Ya kuma bukaci iyaye da su ja kunnen ‘ya’yan su, yana gargadi cewa gwamnatin jihar za ta fara aiwatar da matakai masu tsauri don yaki da masu aikata laifukka.

“Iyaye su gargadi ‘ya’yan su. Daga yanzu, da wuta ake mayar da martani,” in ji Bago. “Haka kuma duk gidan da aka samu yana boye masu laifi, za a rushe shi, jihar Neja ba wurin banza bane.”

Duk da cewa Gwamna Bago bai bayyana a fili cewa dreadlocks ko weavon na da alaka da aikata laifukka ba, ya nuna cewa irin wannan fita tana nuna wata alama ta rashin da’a da ke taimakawa wanzuwar rashin tsaro a jihar.

Wannan umarni ya jawo suka daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam, wadanda suka ce hakan na nuna tauye ‘yancin mutum da kuma yiwuwar amfani da shi wajen cin zarafi a wurin jami’an tsaro.

Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto a ranar Talata, babu wata sanarwa a hukumance daga Gwamnatin jihar Neja, da ta fayyace manufar wannan doka ko ta mayar da martani kan martanin da aka samu.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *