October 16, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnan Jihar Zamfara Ya Biya Naira Biliyan 9 Ga Ƴan Fansho.

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Gwamnan jahar Zamfara da ke Arewacin Najeriya, Dauda Lawal, ya biya N9,357,743,281.35 a matsayin kuɗaɗen gratuti da ma’aikatan da su ka yi ritaya a jahar Zamfara ke bi bashi tun daga 2011.

Gwamnan ya amince da fara biyan kuɗaɗen ne a watan Fabrairun bana.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Asabar a Gusau, ya bayyana cewa gwamnati ta biya ma’aikatan jihar da suka yi ritaya N4,860,613,699.22 a cikin rukuni tara.

Sanarwar ta ƙara da cewa an biya maƙudan kuɗaɗe har Naira miliyan dubu 4,497,129,582.13 ga ma’aikatan ƙananan hukumomin jahar da su ka yi ritaya ko subka rasu.

Ya ce: “A cikin ƙudirin sa na sake fasalin ma’aikatan gwamnatin jahar Zamfara, a watan Fabrairu Gwamna Lawal ya kafa kwamitin da zai tantance ‘yan fansho na jahar da ba a biya su kuɗin gratuti ba tun daga 2011.

“Ya zuwa yanzu mutane 2,666 daga cikin 3,880 da aka tantance masu karɓar fansho, an biya su jimillar kuɗaɗen su na gratuti, wanda ya kai N4,860,613,699.22, daga cikin haƙƙoƙan su da gwamnatocin baya basu biyasu ba. An biya waɗannan kuɗin ga waɗanda suka yi ritaya tsakanin 2015 zuwa 2024″ inji shi.

Ba ƙwace motocin sojoji ƴan bindiga su ka yi ba – Mazauna Zamfara.

Ba ƙwace motocin sojoji ƴan bindiga su ka yi ba – Mazauna Zamfara.

Kwanakin Bello Turji Sun Kusa Ƙare Wa- Sojin Najeriya.

Ya kara da cewa “A ɗaya ɓangaren kuma, an biya mutane 3,840 daga cikin 4804 da aka tantace na ma’aikatan ƙananan hukumomi da malaman firamare da suka yi ritaya N4,497,129,582.13 a cikin rukuni tara. Cikakkun kuɗaɗen da ƙananan hukumomi ke bi ya kai N5,688,230,607.20, daga ciki kuma an biya N4,497,129,582.13 zuwa yau. Wadanda suka ci gajiyar biyan su ne waɗanda suka yi ritaya tsakanin 2011-2021″.

“A taƙaice, ya zuwa yanzu jahar ta biya jimillar N9,357,743,281.35 a matsayin gratuti daga cikin jimillar N13,784,179,513.80 da ake bin jahar zuwa adadin 6,506 da aka tantance masu cin gajiyar ritaya daga cikin 8468 da aka tantance, ma’aikatan da suka yi ritaya.

Waɗanda suka ci gajiyar biyan su ne ma’aikatan da suka yi ritaya tsakanin 2011-2024.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *