February 23, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da murabus ɗin kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da Tabbatar da Nagartar Aiki Injiniya Mahammad Diggol.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

An dai naɗa Muhammad Diggol a matsayin kwamishinan sufuri a farkon gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf a shekarar 2023.

Daga baya gwamnan ya mayar da shi Ma’aikatar Bibiya da Tabbatar da Nagartar Ayyuka, in da ya yi aiki har zuwa wannan lokaci da ya yi murabus.

Sallamar da Gwamna Abba ya yi wa Sakataren Gwamnati da Kwamishinoninsa 5.

Gwamnan Kano ya gana da ƴan majalisar wakilai na Kano Kano sabuwar dokar haraji.

Gwamnan Abba ya zargi gwamnatin Ganduje da cin hanci da rashawa da gazawa wajen tsara birane.

Gwamna Yusuf ya bayyana godiyarsa ga Engr. Diggol bisa hidimarsa da jajircewa gami da sadaukarwar da ya yi a lokacin da ya ke matsayin dan majalisar zartarwa ta jiha.

A cewar sanarwar, Gwamnan ya kuma mika sakon fatan alheri ga Engr. Diggol a cikin al’amuran rayuwarsa ta gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *