Daga Sani Ibrahim Maitaya.
Gwamnan jihar Yobe da ke Arewacin Najeriya, Mai Mala Buni, ya amince da biyan mafi karancin albashi na naira 70,000 ga ma’aikatan jihar, daga watan Disamba 2024.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai na gwamnan Mamman Muhammad, ya fitar wanda ya rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce, amincewar ta biyo bayan shawarwarin kwamitin mafi karancin albashi wanda sakataren gwamnatin jihar Alhaji Baba Mallam Wali ya jagoranta.
Gwamnatin Yobe ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar
Atiku ya ja kunnen shugaba Tinubu kan ciyo wa Najeriya bashi.
Kwamitin ya kuma ba da shawarar daidaita kuɗaɗen ƙananan hukumomi domin tabbatar da an samu sauyi cikin sauƙi zuwa sabon tsarin mafi ƙarancin albashi na ma’aikatan ƙananan hukumomin, wanda tuni aka fara shirye shiryen aiwatar da shi kuma nan ba da jimawa ba za a miƙa shi don amincewa.
Daga bisani kuma Gwamnatin Jihar ta buƙaci ma’aikatan da su kasance masu rama halarci yayin gudanar da ayyukan su.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Kuɗin hutu na 2024: Ma’aikatan Soba sun yabawa shugaban ƙaramar hukumar bisa biyansu akan lokaci.
-
Kwastam za ta ɗauki sabbin ma’aikata 3,927 a Najeriya.
-
Gobara ta ƙone kasuwar Babura ta Yar-Dole da ke jihar Zamfara.
-
Matatar Dangote haɗin gwiwa da kamfanin mai na MRS za su sayar da fetur a kan N935 duk lita.
-
Sojojin Nijar sun kashe Mahara 29 a Tillaberi.