Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cafke Akanta Janar na jihar Sirajo Jaja, da jami’an Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) suka yi, bisa zargin almundahanar Naira biliyan 70, a matsayin wani yunkuri na kutunguilar ’yan adawa da kuma siyasa.
Jaridar LEADERSHIP ta ruwaito cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kama Jaja tare da wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, wato Aliyu Abubakar na Jasfad Resources Enterprise wanda ba a yi wa rajistar harkokin canjin kudi (Bureau de Change) ba, da kuma Sanusi Ibrahim Sambo mai sana’ar POS.
EFCC ta yi zargin cewa Jaja ya cire kudi har Naira biliyan 59 daga asusun bankuna daban-daban da ya bude kuma yake tafiyarwa.
Hukumar ta kuma ce tana gudanar da bincike kan Gwamna Mohammed dangane da lamarin.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Kwamared Mukhtar Gidado ya sanya wa hannu, kuma aka rabawa ’yan jarida a Bauchi, gwamnan ya ce yana da masaniya kan rawar da Ofishin Akanta Janar na jihar ke takawa a cikin zargin da ake yi.
Ya jaddada cewa “Dole ne mu nuna cewa wannan batu yana karkashin bincike mai zurfi da Hukumar Yaki da Cin Hanci ta jihar Bauchi ke yi.”
Gwamna Mohammed ya kara da cewa, “EFCC na da cikakken sani kan wannan bincike da ake yi, wanda ya kai ga daukar matakai masu tsauri ciki har da cirewa, da cafkewa da kuma binciken tsohon Akanta Janar na jihar da wasu manyan sakatarori da dama.”
Ya ce ba za a yarda wani jami’in gwamnati ya fuskanci cin zarafi ko kuma a take masa hakkin sa ba.
“Gwamnatin jihar za ta bi duk wata hanya ta shari’a da kundin tsarin mulki ya tanada, domin kare jami’anta daga cin zarafi ko zalunci.” inji shi.
Ya ce ya samu labarin cafke Jaja cikin mamaki, duba da cewa lokacin da aka kama shi yana Abuja ne yana gudanar da aikin sa na halartar taron Hukumar Rabon Kudin Tarayya watau ‘FAAC meeting’.
“Yanzu da dama daga cikin ‘yan Najeriya na kallon wannan a matsayin siyasa kawai ba wai kokarin yaki da cin hanci da rashawa ba. Lokaci da kuma yanayin cafke shi ya sa ake shakku kan hakikanin manufar lamarin”. Inji sanarwar.
“Gwamnatin jihar Bauchi ta dade tana nuna jajircewar ta wajen gudanar da gaskiya, rikon amana da bin doka. An bayyana gwamnati na a matsayin daya daga cikin gwamnatoci mafiya gaskiya a fannin tafiyar da kudaden jama’a”.
“Muna gudanar da harkokin gwamnati bisa gaskiya da bin doka. Tarihin mu ya nuna haka, kuma za mu ci gaba da aiwatar da nagartaccen shugabanci,” in ji shi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja