September 22, 2021

Gwamnatin Bauchi zatayi rejistan filaye samada dubu dari acikin kasada watanni Biyar : Kwamishinan Filaye da Safiyo. 

Page Visited: 180
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 15 Second

An bukaci masu sarautun gargajiya dama sauran masu Ruwa da tsaki a yankin Kasar Hakimin Miri da Kuma Tirwun dasu cigabada bada dukkanin goyon baya data dace domin cimma kudurin gomnati na sauya fasalin hanyoyin guda biyu dake wajen garin Bauchi da zummar ganin cigaban yankunan.

 

Kwamishinan Ma’aikatar Filaye da safiyo Farfesa Adamu Ahmed shine ya bayyana hakan a wajen taron masu Ruwa da tsaki, Jami’an tsaro harma da jami’ai daga Hukumar kulada bunkasa cigaban jihar Wanda taron ya gudanarda anan Bauchi.

 

Adamu Ahmed yace jihar Bauchi itace Birni daya tilo da tafi bunkasa a yankin shiyar Arewa maso gabas, adon haka saiya bukaci da’a samarda kyakkyawan alaka atsakanin tsakanin ma’aikatar da kuma sauran bangarori domin cimma kudurorin da kuma shirye shiryen gomnati.

 

Yace gomnatin jihar Bauchi ta himmatu wajen ganin ta samarda ayyukan cigaba a fadin jihar ta hanyar wayardakan masu Filaye a wannan jihar.

 

Adamu Ahmed ya kuma bayyana kudurin ma’aikatar na ganin ta fara aiwatarda rejistan filaye a wannan jihar ta hanyar tallafi data samu daga bankin duniya, inda ake saran za’ayi rejistan filaye samada dubu dari acikin kasada watanni Biyar.

 

Ya kuma bayyana bukatar dake akwai ga masu filaye dasuyi aiki da kuma bin doka, ta hanyar neman izini daga Hukumar kulada bunkasa cigaban jihar Bauchi.

 

Anashi jawabin, Hakimin kasar Miri Malam Hussaini Abubakar Othman yasha alwashin bada goyon baya daga bangaren masu sarautun gargajiya wa gwamnatin jihar domin cimma shirye shiryen samarda ayyukan cigaba a fadi n jihar Bauchi.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us