January 31, 2023

Gwamnatin Buhari ta gaza kan matsalar ASUU – Kungiyar CNG

Page Visited: 519
0 0
Read Time:2 Minute, 5 Second

Daga Muhammad Sani Mu’azu

 

Wani Malamin jami’a anan Bauchi Parfesa Dalhat Bala Sulaiman ya zargi gazawar Gwamnatin Tarayya amatsayin silar cigaba da kasancewar Jami’oin kasar Nan a rufe.

Dalhat Bala Sulaiman yayi Batun ne yayin Wani Babban taro Wanda ya hada hancin shuwagabannin dalibai, iyaye, da kungiyoyin fafutuka, kan ci gaba da fuskantar yajin manyan makarantun kasar Nan da kungiyoyin ASUU da COEASU ke ci gaba da gudanarwa a fadin kasa.

Acewar Farfesa Dalhat Bala Sulaiman, gwamnatin Buhari ta gaza wajen magance yajin aikin ASUU da yaki ci yaki cinyewa, musamman kan lamarin kudaden gyara makarantu da kuma tsarin biyan albashi na IPPIS.

Ya kara da cewa matukar gwamnati ta bada kulawa wa bangaren ilimi kwatankwacin wanda ta bayar a babban taron jam’iyya da ya gabata babu makawa bangaren zai inganta.

Shima da yake jawabi, shugaban kungiyar Malaman kwalejojin kimiyya da fasaha ta kasa reshen kwalejin koyon aikin gona ta jihar Bauchi Comrade Nuhu Abubakar yace Malaman makarantu suna fuskantar kalubale da dama, yana mai bada misali da rashin dabbaka karin girma wa ma’aikatan jihar Bauchi na tsawon shekaru biyar da suka gabata.

Yayi kira ga dalibai da su fahimci fafutukar malaman makarantu a fadin kasar domin ba a sonsu yajin aikin ke ta’azzara ba.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban kwalejin koyon aikin gona na jihar Bauchi Dr. Shehu Abdulkadir Zailani ya bayyana cewa mafi yawan batutuwan da kungiyoyin ke fafutuka akai suna kan hanya inda yayi kira ga bangarorin biyu da su sassauto, don nemo maslaha ta dindindin don amfanin dalibai.

Acewarsa, mafi yawan wadanda ke rike da madafun iko a kasar nan sun mori ilimi kyauta a amma a yanzu suna yunkurin kirkiro da biyan kudin Makaranta inda yayi kira ga kungiyoyin dalibai da kadansu yarda da hakan ta kowanne hali.

Wacce uwa da ta halarci taron Briskila Emefesi ta shawarci dalibai da su nemi sana’oin dogaro da kai domin a yanzu haka babu ayyukan gwamnati a kasa.

Wanda ya kira taron, wanda kuma shi ne mataimakin sakataren hadakar kungiyoyin Arewa reshen dalibai Comrade Ibrahim Abdullahi Soro ya ce makasudin shirya taron shi ne don a tattauna lamuran da ke jawo ta’azzarar yajin aikin kungiyoyin ASUU da COEASU don nemo maslaha na dindindin.

Ya zargi gwamnatin tarayya bisa lalacewar bangaren ilimi, yana mai cewa dalibai basu da wani zabi da ya wuce su dauki matakin da zai tursasawa gwamnati zama a teburin sulhu da kungiyar ASUU.

Yayi kira ga masu sarautun gargajiya da Malaman addini da su shiga lamarin don ceto bangaren ilimi daga rugujewa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *