Daga Abdul`azez Abdullahi
Majalisar Zartaswar Jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya CON, ta amince da Naira biliyan 4 da miliyan 205 don biyan kuɗaɗen sallama ga ma’aikatan jiha 2,204 da suka yi ritaya a 2019 da 2020.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwmamnan Isma`ila Uba Misille ya fita ta ce mataimakin gwamnan jihar, Dr. Manassah Daniel Jatau, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai bayan taron majalisar zartaswar jihar.
Dokta Jatau yace amincewar ta biyo bayan nasarar da aka samu ne na biyan giratututin 2014 zuwa 2018, wanda ya haura Naira biliyan 13, ga tsofin ma’aikata 5,658 a matakin jiha da kuma tsofin ma’aikata 6,027 a matakin ƙananan hukumomi.
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
An yi arangama tsakanin makiyaya da manoma a jihar Gombe.
Ya ƙara da cewa tun farkon gwamnatin Gwamna Inuwa Yahaya, ta biya basussukan giratututi ga ma’aikatan da su ka yi ritaya a matakin jiha da ƙananan hukumomi, wanda ya kai Naira biliyan 17 da miliyan 235.
Mataimakin Gwamnan ya jaddada ƙudurin gwamnatinsu na ci gaba da biyan kuɗaɗen giratututi da fansho a matsayin ƙoƙarin da ba a saba gani ba, in da ya banbanta kanta game da rashin kulawar da ‘yan siyasa ke yiwa tsofin ma’aikata a faɗin ƙasar nan.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.
-
Jami’an tsaro sun ragargaza Lakurawa a jihar Kebbi.
-
Matatar Man Dangote ta ƙulla yarjejeniya da wasu kamfanoni don karya farashin man fetur a Najeriya.
-
Me Shamsiyya ta aikata `Yansanda Kano su ka kama ta da abokanta?