Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Gwamnatin Kano ta binciki matsalar zaizayar ƙasa a Sheka, Guringawa da Wailari - Martaba FM Gwamnatin Kano ta binciki matsalar zaizayar ƙasa a Sheka, Guringawa da Wailari - Martaba FM

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Gwamnatin Jihar Kano ta fara bincike kan matsalar zaizayar ƙasa da ke barazana ga lafiyar jama’a da kadarori a yankunan Sheka Guringawa da Wailari Yan Lemo na ƙaramar hukumar Kumbotso.

Kwamishinan Ma’aikatar Muhalli da Sauyin Yanayi, Dr. Dahir M. Hashim, ya jagoranci wata tawaga ta ƙwararru domin gudanar da cikakken bincike da tattara bayanai da za su taimaka wajen ɗaukar matakan da suka dace don shawo kan matsalar.

A cewar Dr. Hashim, wannan binciken na daga cikin yunƙurin Mai Girma Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na tabbatar da kare lafiyar al’umma da kuma samar da muhalli mai inganci ga mazauna jihar.

“Mun ziyarci wuraren da abin ya shafa tare da ƙwararrun injiniyoyi da masana, domin tantance girman matsalar da kuma hanyoyin da za a bi don magance ta cikin gaggawa,” in ji kwamishinan.

Ya ƙara da cewa gwamnati za ta ci gaba da sa ido kan irin waɗannan matsaloli a fadin jihar tare da ɗaukar matakan kariya tun kafin su haifar da mummunar illa.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *