Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Majalisar zartarwa ta gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta amince da dawo da sunan Northwest University ga jami’ar Yusuf Maitama Sule, wanda aka sauya suna a baya.
Cikin wata sanarwa da kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jihar Kano Dr. Yusuf Kofamata ya wallafa a shafinsa na facebook ya ce, “majalisar ta amince maidawa da jami’ar sunanta na asali wato Northwest University Kano.
“Kazalika majasar zartarwar ta amince a sanya sunan na Yusuf Maitama Sule a sabuwar Kwalejin ilimi ta ƙaramar hukumar Ghari domin girmamawa ga mai sunan”, in ji Kwamishinan.
Sama da ɗalibai dubu 12 ne suka zana jarrabawar neman shiga Jami’ar Yusuf Maitama da ke Kano.
ASUU ta nuna damuwa kan yawaitar ɗaliban da ke samun sakamakon first-class a Najeriya.
Shugaban Faransa ya yabawa Tinubu kan inganta ci gaban Najeriya.
Kofarmata ya kuma bayyana cewa tuni aka bayar da umarnin tura waɗannan dokoki zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano domin zamar da su doka, ciki har da gyaran dokar shekarun aiki na manyan makarantu daga shekaru 65 zuwa 70 ga farfesoshi na jami’a, da kuma 60 zuwa 65 na sauran manyan makarantu.
Idan ba ku manta tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ne ya canza makarantar suna daga Northwest University zuwa Yusuf Maitama Sule a lokacin da ya ke kan mulki.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
“Kwararar masu aikata laifuka daga jihohin makwabta ne abin da ya taimaka wajen ƙalubalen tsaro”- Gwamnatin Gombe.
-
Kano da Katsina, sun zama a sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kuɗi.
-
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
-
Ƙungiyar Alkalai sun shiga yajin aikin sai baba ta gani.
-
NAFDAC ta gargaɗi masu gidajen Burodi kan amfani da Sakarin.