Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ba da kyautar filin da ke kusa da gidan Qadiriya a unguwar Kabara ga Qadiriya domin yin zikiri.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen hawa ta Kano, KAROTA, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar a ranar Talata.
Baffa Babba Dan’agundi, Manajan Darakta na KAROTA, wanda ya zama shugaban kwamitin rushe haramtattun gine-gine ne ya samar da haka a cikin sanarwar.
Gwamna Ganduje ya ba da umarnin katange tare da fitar da wuraren wasanni na yara a filin, yayin da sauran wuraren kuma yace a bar shi a matsayin Filin da Yan Kadariyya za su yi amfani da shi wajen yin zikiri.
Hakan ya biyo bayan umarnin gwamnatin Kanon na ba da umarnin rushe wani katafaren gini a filin da ke kusa da gidan Sheikh Nasiru Kabara da ke cikin birnin jihar.
Gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ne ya bayar da umarnin rusau ɗin, bayan da bincike ya nuna cewa ana yin ginin ne ba tare da izini ba a hukumance.
Kuskure Ne Rufe Titi A Yayin Sallar Juma’a, Cewar Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara.
Tin da fari sanarwar ta ce, da fari gwamnatin Kano da masarautar su na ta zargin juna kan ko ɗaya da ga cikin su ne ya bada izinin ginin, ya kara da cewa sai da aka gudanar da bincike sai a ka gano ba haka bane.
Daman tinda daɗewa mabiya ɗarikar Ƙadiriya na taruwa duk sati a kusa da filin domin yin zikirin Juma’a da sauran wasu tarurruka ƙarƙashin jagorancin shugaban ɗarikar na Afirka Sheikh Abdulƙadir Qaribullahi Sheikh Muhammad Nasiru Kabara.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Har yanzu ina matuƙar son Buhari, in ji fasinjan da ya kuɓuta daga hannun ƴan bindiga.
-
Hana Acaɓa A Jihar Bauchi: Abubawan Da Ake Musu Gaskiya Ba Da Hannun Gwamnatin jihar Bauchi Bane, -Gwanma Bala.
-
KAROTA Ta Kama Wani Matashi Da Ke Sojan Gona Da Sunanta.
-
Kungiyar Mawakan Sahwa Da Aka Yaɗa Mutuwar Su Sama Shekaru Goma Za Su Gana Da Ƴan Najeriya Ranar Asabar.
-
Mawakan Sahwa Ƴan Ƙasar Sudan Da Aka Yaɗa Mutuwarsu Sama Da Shekaru 10 Suna Nan A Raye.