December 2, 2021

Gwamnatin Kano Tace Zai Yi Wahala A Samar Da Ruwan Sha A Jihar.

Page Visited: 367
0 0
Read Time:45 Second

Hukumar bada ruwan sha ta jihar Kano ta ce , zai yi wahala a samar da ruwan sha a kowane lungu da sako na jihar.

Shugaban hukumar Injiniya Garba Ahmad Kofar Wambai,ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin ziyarar da mataimakan Gwamna na musamman suka kai hukumar.

“Zai yi wahala a samar da ruwan sha a kowanne lungu da sako na jihar ko da kuwa za’a yi amfani da duka kudaden gwamnati wajen magance matsalar rashin ruwan ” a cewar shugaban hukumar.

Ya kuma ce hakan ya biyo bayan faɗaɗa da jihar ke yi ne, “saboda girma da faɗaɗa da jihar ke yi a kullum ne ya sanya ba za’a taba kawo karshen matsalar ruwan sha ba”.

Sai dai ya tabbatar da cewa, za su yi duk mai yiwuwa wajen habaka harkar bada ruwan shan.

Wannan na zuwa ne yayin wasu yankuna a jihar ke fama da matsanancin rashin ruwan sha.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *