Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Gwamnatin jihar Kano ta kafa wani kwamitin ƙwararru da zai yi aikin yi wa baƙi ƴan ƙasashen waje mazauna birnin rijista musamman waɗanda suke gudanar da kasuwanci.
BBC ta rawaito gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne domin samun alƙaluman mutanen da suka fito daga ƙasashen ƙetare kuma suke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar, ta yadda za a haɓɓaka kudin shiga da kuma tsaro da samar da ayyukan yi.
APC Ta Gargaɗi Gwamnan Kano Kan Gudanar Da Zaɓe Ƙananan Hukumomi Gobe Asabar.
Rashin adalci ne a bada rabon tallafin shinkafar Kano a hannun APC – Kwankwaso.
Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.
Kwamitin wanda ke ƙarƙashin ofishin sakataren gwamnatin Kano, zai tattara bayanan baƙi ƴan ƙasashen waje da ke aiki walau na kamfani ko a wata ma’aikata ko kuma kasuwanci.
Shugaban kwamitin, Lawan Isa Kibiya ya ce aikin da za su yi zai taimaka wajen tabbatar da ganin baƙin waɗanda mafi yawa ƴan kasuwa ne su na biyan haraji kamar yadda doka ta yi tanadi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP