Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Gwamnatin Kano za ta gyara gine-ginen masallatan Juma'ar jihar. - Martaba FM Gwamnatin Kano za ta gyara gine-ginen masallatan Juma'ar jihar. - Martaba FM

Gwamnan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya Abba Kabir Yusuf, ya bayyana aniyar gwamnatin sa na gyara dukkan manyan masallatai na Juma’a a fadin jihar, domin tabbatar da cewa sun dace da matsayin da ya kamata ga masu ibada.

Gwamna Abba ya bayyana hakan ne a ranar Asabar, yayin da ya karɓi bakuncin manyan membobin Majalisar malammai da limamai domin yin buɗa baki a Fadar Gwamnati, a kwanaki 15 na Ramadan.

Ya umarci Kwamishinan Harkokin Addini da ya tattara jerin masallatan da ke buƙatar gyara cikin gaggawa, domin gwamnati ta ɗauki matakin da ya dace.

Bugu da ƙari, gwamnan ya bayyana cewa ana gina sabon Masallacin Juma’a a cikin Fadar Gwamnati mafi girma, domin ya ɗauki masu ibada da yawa tare da haɓɓaka ayyukan addini.

Gwamna Yusuf ya nuna matuƙar godiya ga addu’o’i, da shawarwari, da gudunmawar da shugabannin addini ke bayarwa, wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano.

Da yake jawabi a madadin shugabannin addinin, Sheikh Muhammad Nasir Adam Limamin Masallacin Sheikh Ahmad Tijjani, ya yaba da hangen nesa na gwamnan, inda ya ce addinin Musulunci na karfafa ciyar da masu azumi da kuma gina wuraren ibada.

Ya tabbatar da goyon bayan malammai da addu’o’in su ga cigaban jihar.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *