Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano a ranar Asabar, ya karɓi bakuncin manyan membobin Majalisar malammai da limamai domin yin buda baki a Fadar Gwamnati, a kwanaki 15 na Ramadan.
Wannan taro ya kasance wata dama don ƙarfafa haɗin kai, girmama rawar da shugabannin addini ke takawa wajen wanzar da zaman lafiya, tare da bayyana manyan ayukka da za su haɓɓaka cibiyoyin addini a jihar.
A yayin taron, Gwamna Yusuf ya bayyana shirin mayar da Filin Sallar Idi na Kofar Mata zuwa Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa ta Addinin Musulunci. Ya bayyana cewa maimakon a bar filin a wofi ko kuma yin amfani da shi ba dai-dai ba bayan salloli biyu na shekara-shekara, zai fi dacewa a maida shi cibiyar addini da za ta kasance wurin gudanar da ayyukan ilimi da wa’azi.
Gwamnan ya jaddada cewa, filin da ake amfani da shi sau biyu kawai a shekara, idan aka mayar da shi Cibiyar Musulunci ta zamani, zai zama wurin da za a ci gaba da gudanar da harkokin ilimi na addini da kuma tattaunawa tsakanin malaman Musulunci.
Ya ƙara da cewa za a yi bikin aza harsashin ginin cibiyar makonni biyu bayan Sallar Idi, sannan a miƙa shi ga majalisar malammai domin kula da gudanarwar sa.
Liyafar buɗa bakin ta samu halartar membobin Hukumar Shari’a, mambobin Majalisar Zartarwa, da wasu fitattun mutane.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja