January 22, 2025

Gwamnatin Kano Za Ta Taimaki Manoma Da Masu Kiwo Cikin Kasafin 2024,- KNARDA.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Ma’aikatar bunƙasa aikin gona ta jihar Kano da ke Najeriya KNARDA ta ce ta shirya taimakawa manoma da masu kiwo nan gaba, kamar yadda shugaban hukumar gudanarwar na ma’aikatar Dr Faruk Kurawa, ya bayyana.

Kurawa, ya bayyana hakan ne a ranar Talata, ya yin da ya karɓi bakuncin wata kungiyar Manoma da ke Kano ta Gida-gida All Farmers Association a turance.

Ya ce, gwamnatin su ta Abba Kabir Yusuf, al’umma suke wa aiki, “duk abinda zai kawowa Kano ci gaba shi muke nema, mu alƙibilar mu al’ummar jihar Kano ne da gyararraki a gaban mu, duk wasu kungiyoyi duk masu manoma, duk abinda za mu yi, mu taimaki mutane za mu yi wannan shine alkawarin da muka yi”.

“Akwai tsare-tsare da zamu yi wanda zamu taimakawa ƙungiyoyin manoma, masu kiwon kaji, masu noman damuna da rani, masu kiwon dabbobi da sauran su duka, kungiyar ku ba za ta zamanto koma baya ba, in ji Kurawa.

Ya kuma ƙara da cewa, “una nan nuna tsare-tsaren kasafin kudi na shekarar 2024 saboda an bamu lokaci mu je mu kammala mu miƙa, to dukkan wasu koke-koke na kungiyoyi yana ciki”.

Tinda farko da yake jawabi shugaban ƙungiyar Abba Hassan Dala, ya ce kungiyar ta kai ziyara ne ga sabon shugaban ma’aikatar domin gabatar masa da ayyukansu da taya shi murna da kuma bayyanawa gwamnati irin tarin matsaloli da Manoma ke fuskanta da yadda za a taimake musu.

“Ƙungiyar mu ƙungiya ce ta ƴan asalin jihar Kano, kuma muna da yaƙinin wannan gwamnati ƙarƙashin jagoranci gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ta zo ne domin ta yi wa Kano hidima, don ci gaban jiha, ba shakka mu gamayya manoma da masu kiwo mun shirya tsaf don mu taimaki manufofin gwamnati saboda mu kawo ƙarshen tilin matsalolin da muke fuskanta,” in Abba Hassan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *