Kasuwanci
Trending

Gwamnatin Najeriya Ta Bai Wa Ƴan Kasuwa Wa'adin Tata Ɗaya Su Rage Farashi.

Hukumar kula da hakkin mai siye ta tarayya FCCPC, ta bai wa ‘yan kasuwa wa’adin wata guda da su rage farashin kayayyakin da suke siyarwa.

Sabon shugaban hukumar, Mista Tunji Bello ne ya sanar da hakan a yayin taro da masu ruwa da tsaki don magance tsawwala farashin kayayyki da ya gudana a ranar Alhamis a Abuja.

Bello ya ce hukumar za ta fara daukar mataki da zarar wa’adin ya cika.

Yayi bayanin cewa an shirya taron ne domin tattauna yadda za a magance hauhawar farashin kayayyaki sake ba kaidi da kuma wasu dabi’u na saba ka’ida da kungiyoyin ‘yan kasuwa ke yi.

Acewarsa, wani bincike da hukumar tayi ya gano yadda ake siyar da Injin markada kayan marmari kan Naira dubu 140 a wani shagon siyar da kaya a birnin Texas, amma a Legas ake siyar da abin kan Naira 944, 999.

Bello, ya bayyana mamaki kan banbancin farashin wanda ya kai yawan hakan.

Shima anasa jawabin, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na birnin tarayya Abuja, Ifeanyi Okonkwo ya ce kudaden da ake caza wajen shigo da kayayyaki a tashoshin jiragen ruwa na taka muhimmiyar rawa wajen hauhawar farashin.

Daily Nigerian Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button