Daga Fatima Suleiman Shu’aibu.
Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta rabawa manoma Irin alkama mai jure zafin rana da yawansa ya kai tan dubu 1 da 500 a bana, ƙarƙashin shirin tallafawa aikin noma kashi na 1.
RFI ta rawaito, shugaban shirin a matakin ƙasa, Ibrahim Mohamed Arabi ne ya bayyana haka, a ziyarar da ya kai wani kamfanin takin zamani a ƙaramar hukumar Madobi ta jihar Kano.
Gwamnatin Najeriya za ta kammala gyaran matatar mai ta Kaduna zuwa ƙarshen Disamban 2024.
Atiku ya ja kunnen shugaba Tinubu kan ciyo wa Najeriya bashi.
EFCC ta gurfanar da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello a Kotu kan almundahana da naira biliyan 110.
Arabi ya ce sabon Irin zai taimaka wajen magance ƙarancin alkama da tsadarta, yayin da a gefe guda zai tallafawa ƙananan manoma.
Ya ƙara da cewa kamfanin Al-Yuma da ke samar da Iri, taki, da sauran kayayyakin noma na Jihar Kano ne zai samar da Irin alkamar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.