October 16, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnatin Tarayya ba za ta saka tallafi a kuɗin aikin Hajjin 2025 ba,-NAHCON.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

A Najeriya hukumar kula da aikin Hajji ta kasar, NAHCON ta ce gwamnati ba za ta ba da tallafin aikin Hajji na 2025 ba.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta fitar bisa aikin Hajjin 2025, ta ce “Babu tsarin rage kudin canji ga biyan kudin aikin Hajji ga Alhazai da ke karkashin jiha ko masu zaman kansu”.

Hakan na nufin idan Dalar Amurka ta ci gaba da zama a Naira 1, 650, kowanne Alhaji zai biya Naira Miliyan 10.

Fadar Shugaban Najeriya Ta Karrama Shugaban Makarantar Sakandare A Jihar Zamfara.

Kuskuren Jaridar Daily Trust Da Yadda Gaskiya Ta Bayyana Game Da Yarjejeniyar Samoa.

Kwanakin Bello Turji Sun Kusa Ƙare Wa- Sojin Najeriya.

A yayin da har yanzu hukumar NAHCON ba ta sanar da kudin aikin Hajjin na 2025 ba, sai dai wasu jihohin sun sanar da Naira Miliyan 8.5 a matsayin kafin Alkalami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *