January 22, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnatin tarayya za ta fara allurar rigakafin zazzaɓin cizon sauro a jihohin Kebbi da Bayelsa a Yau.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta ƙasa NPHCDA ta ce kashi na farko na shirin rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauro a Najeriya zai fara ne a jihohin Kebbi da Bayelsa.

cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin ta na X hukumar ta ce rigakafin cutar zazzaɓin cizon sauron zai kasance wani bangare ne na yaƙi da zazzaɓin cizon sauro a Najeriya, wanda zai ba da kariya ga miliyoyin yara da kuma kusantar da ƙasar nan zuwa makomar kawar da zazzabin cizon sauro.

Daily Trust ta rawaito, a farkon watan Oktoba ne dai gwamnatin tarayya ta karɓi allurai miliyan ɗaya na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro mai nau’in R21/ wanda ƙungiyar nan da ke bayar da gudummawa wajan yaƙi da zazzaɓin cizon sauro wato Gavi, ta bayar, tare da tallafin Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF haɗin gwiwa da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO).

“Mun himmatu wajen gina Najeriya mai cike da inganci” bayan hana ƴan Najeriya yin rayuwa ƙarya- Tinubu.

Shugaba Tinubu zai wuce ƙasar Afirka ta Kudu daga Faransa.

“Bai kamata tsare- tsaren kuɗi da gwamnati ke son ingantawa ya fifita wasu jihohi ƙalilan ta hanyar ruguza sauran ba”- Atiku Abubakar.

Babban Darakta a Hukumar kula da lafiya matakin farko na kasa Dr Muyi Aina, ya ce za a yi wa yara ‘yan watanni biyar zuwa watanni 15 allurar rigakafin a matsayin wani ɓangare na rigakafi na Yau da Kullun.

“Za kuma a faɗaɗa Shirin zuwa wasu jihohi kuma a haɗa shi cikin jadawalin rigakafi na Yau da Kullun na ƙasa, yayin da ake ci gaba da karɓar ƙarin allurai.

“Kashi na biyu zai shafi jihohi 19 da babban birnin tarayya Abuja, yayin da kashi na uku kuma zai shafi sauran jihohi 15. An tsara dukkan matakan biyu domin 2025, ”in ji shi.

Anasa bangaran Daraktan rigakafi da hana yaɗuwar cututtuka na hukumar kula da kiwon lafiya matakin farko na jihar Kebbi, Junaidu Haliru Gwandu, ya ce jihar ta yi wa yara 595,000 rigakafin allurar zazzabin cizon sauro a matakin farko.

Dokta Walter Mulombo, wakilin WHO a Najeriya, ya ce, “Muna da yaƙinin cewa wannan allurar rigakafin tare da sauran matakan kariya, zasu rage raɗaɗin zazzaɓin cizon sauro a Najeriya matuƙa, kuma zai taimaka wajan cimma burin mu na kawar da cutar zazzaɓin cizon sauro Afirka.”

Masana kimiyya a Jami’ar Oxford ne suka kirkiro maganin Mai nau’in R21 kuma Cibiyar Serum ta Indiya da Novavax suka ai watar dashi

Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen Duniya da su ka goyi bayan alurar riga kafin na zazzaɓin cizon sauro domin ganin an kare yara kaɗai.

Cutar zazzabin cizon sauro na ɗaya daga cikin cutukan da suka fi hallaka mutane a Najeriya, in da ke kashe dubban daruruwan yara ‘yan kasa da shekaru 5 a kowace shekara.

Najeriya ce ke da kusan kashi 27% na cutar zazzaɓin cizon sauro a duniya da kuma kashi 31% na mace-mace a dalilin zazzaɓin cizon sauro a duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *