Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta amince da sayo jiragen yaki masu saukar unguku har guda 12, domin tunkarar matsalar tsaro da ta dade tana addabar kasar nan.
Rundunar sojin Nijeriya za ta yi amfani da jirage yakin masu saukar ungulu ne wajen yin sawagi a sasarin samaniya domin magance kalubalen tsaro da ke addabar kasar nan.
Babban hafsan sojin Nijeriya, Laftanar-Janar Taoreed Lagbaja, shi ya bayyana haka a wajen bude taron kara wa juna sani na harkokin jiragen sama na sojojin Nijeriya da ya gudana a Abuja.
Ya ce, jirage masu saukar ungulu guda 12 za su fara aiki da sashin kula da zirga-zirgar jiragen sama na sojojin Nijeriya, wanda aka kafa domin inganta karfin sojojin kasa da daukar dawainiyar aiki da kuma inganci yayin gudanar da ayyuka.
Ya kara da cewa za su ci gaba da bayar da gudunmuwa ga hadakar sojin Nijeriya har sai an samu nasara.
Ya kuma yaba wa shugaban kasar kan yadda ya siya wa rundunar sojojin Nijeriya makamai da sauran kayayyakin aiki domin samun ingantacciyar sashin kula da jiragen sama wanda zai tallafa wa sojojin kasa wajen mai da hankali kan dabarun aiki da zai ba su nasarar dakile matsalar tsaro a kasar nan.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.