September 22, 2021

Gwamnonin Arewa Sun Gana Da Buhari Kan Tsaro.

Page Visited: 118
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:42 Second

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da wasu gwamnonin arewa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

An kira taron ne don tattaunawa kan matsalar tsaro a jihohin arewa 19.

Yayin da yake zantawa da manema labarai bayan taron, gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya ce sannu a hankali zaman lafiya na dawowa yankin sakamakon tsarin tsaro da gwamnatin tarayya da na jihohi suka amince da shi.

A kan ganawar da shugaban kasa, gwamnan ya ce, “Mun tattauna batun tsaro, ba don jiha ta ba kawai ba, face yankin Arewa baki daya, saboda yadda matsalar ta yi kamari a yanzu.

A cewarsa “Na yi masa bayani kuma gwamnan Neja shi ma ya yi masa bayani, shugaban kasar ya tabbatar mana da cewa za a dauki mataki a kan abin da muka tattauna game da batun rashin tsaro. ”

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us