Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa dakta Hakeem Baba-Ahmed ya ajiye aikin sa.
A cewar wani rahoto daga wata jaridar ƙasa da aka fitar a ranar Jumma’a, Baba-Ahmed wanda tsohon mai magana da yawun Northern Elders Forum ne, ya miƙa da takardar murabus din sa kimanin makwanni biyu da suka gabata, sai dai har zuwa lokacin da aka fitar da rahoton, ba a tabbatar da ko fadar shugaban ƙasa ta amince da murabus ɗin a hukumance ko a’a ba.
Ko da yake ba a bayyana dalilan murabus ɗin ba a fili, majiyoyi sun nuna cewa ya yi hakan ne bisa raɓin kan shi.
Zaman sa a fadar shugaban ƙasa bai wuce ba tare da cece-kuce ba, Matsayin sa musamman dangantakar sa da NEF ya jawo suka daga wasu sassa, ciki har da Ministan ƙasa a ma’aikatar harkokin Tsaro Bello Muhammad Matawalle.
A watan Afrilu 2024 Matawalle ya soki wasu daga cikin ‘yan Arewa da aka naɗa muƙamai da cewa, sun yi shiru wajen kare gwamnatin Tinubu daga masu suka; maganar sa ta zama kamar martani kai tsaye ga Baba-Ahmed, wanda ya tsaya tsayin daka wajen kare NEF bayan ƙungiyar ta bayyana cewa yankin Arewa ya yi kuskure da zaɓin Bola Tinubu a 2023.
A martanin sa, Baba-Ahmed ya ce maimakon Matawalle ya riƙa kai hari ga NEF, ya kamata ya fi mayar da hankali wajen bayyana nasarorin sa a gwamnatin.
Ya rubuta cewa:
“Caccakar NEF da Matawalle karamin ministan tsaro ya yi, abin kunya ne kuma bai dace ba; ya kamata ya fi mayar da hankali wajen haskaka gudunmuwar da ministocin Arewa da sauran masu rike da mukamai iri-na, ke bayarwa wajen inganta tsaro da rage talauci a Arewa.”
Sai dai Matawalle ya mayar da martani, inda ya jaddada cewa kowanne wanda aka nada a gwamnati yana da nauyin kare ta.
Ya ce “A matsayin dakta Baba-Ahmed na ɗan majalisar zartaswar gwamnati, yana da nauyin kare nasarorin gwamnati da kuma kare ta daga hare-haren da ba su da tushe, musamman daga waɗanda ke fakewa da kabilanci ko son zuciya wajen hura wutar rikici.”
Ya ƙara da cewa “Duk wani mai mukami a gwamnatin Shugaba Tinubu, ciki har da dakta Baba-Ahmed, yana da nauyin yada ayukkan alheri na gwamnatin da kuma kare kyawawan manufofin ta.”
An haifi Baba-Ahmed a ranar 11 ga watan Satumba 1955 a jihar Kaduna, ya taka rawar gani a aikin gwamnati tun kafin ya yi murabus, ya taɓa zama Sakataren Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) kafin ritayar sa; sannan kuma ya yi aiki a matsayin Shugaban Ma’aikata ga tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki a Majalisa ta 8.
Ya yi karatu a Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, da London School of Economics, da kuma University of Sussex a Birtaniya, inda ya sami digirin digirgir (PhD).
Baba-Ahmed ya fara aiki a matsayin malami a Jami’ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato, kafin ya koma aikin gwamnati a jihar Kaduna, daga nan kuma zuwa gwamnatin tarayya, inda ya kai matsayin babban Sakatare a ma’aikatu da dama, ciki har da Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu.
Ya samu lambar yabo ta kasa Officer of the Federal Republic (OFR), Baba-Ahmed ya shahara wajen fafutukar sauya tsarin mulki da kare muradun Arewa. Kafin ya shiga gwamnatin Tinubu, shi ne Daraktan Yada Labarai da Wayar da Kai na NEF, inda ya shahara da yin magana kan manufofi da ake ganin suna cutar da Arewa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Masu garkuwa da mutane sun nemi kuɗin fansa na Naira miliyan 100 domin sakin Fasto a jihar Kaduna.
-
Jami’an tsaro a Zamfara sun ƙaddamar da farautar Ƴanbindiga a wani yankin jihar bayan sun yi ajalin mutum biyu tare da sace wasu 26.
-
Gwamnatin Cross River ta gargadi shugabannin ƙananan hukumomin jihar kan biyan albashin malaman makaranta.
-
Babban Bankin Najeriya ya samun ƙarin kuɗaɗen shiga da ya kai dala biliyan 6.83 a shekarar 2024.
-
Peter Obi ya gode wa Ƴansanda kan janye gayyatar da su ka yi wa Sarki Sunusi.