August 8, 2022

HARAMTA ACABA A BAUCHI: Abun A Yaba Ko Ayi Allah Wadai?

Page Visited: 479
1 0
Read Time:1 Minute, 30 Second

Daga: Adamu M Abdullahi.

Wasu suna yabawa bisa hukuncin da gwamnatin jihar Bauchi ta yanke na haramta ayyukan acaba a fadin jihar, bisa tsammanin wai hakan zai kai garin Bauchi matsayi daya da sauran manyan birane.

Saidai idan akayi duba na tsanaki wa tsarin za’a gane cewa hanyar da aka bi ba mai bullewa ba ne, kuma ba’a yi dogon nazari ba kafin yanke hukuncin, duba da cewa mafi yawan al’ummar jihar talakawa ne. Dan haka ba karamin zalunci ba ne a toshe hanyar cin abincin dubban jama’ar jihar ba tare da nema musu wata mafita ba.

A fili yake cewa ayyukan acaba na jawo cinkoso a cikin gari da yawaitar hadura kuma bata gari musamman barayi sun fi kai hari ga masu aikin acaba, amma wannan bai kai ya zama dalilin haramta acaba a dare daya ba.

Haba Dan gari! Ta yaya zaka yi wasa da sana’a daya tilo na talakan da zabo ka? Wannan shi ne abun da kayi alkawari a lokacin yakin neman zabe?

Ba zamu iya kau da ido kan muhimmiyar gudumawa da masu acaba ke bayarwa ba na samar da saukakakkiyar hanyar sufuri a kullum.

Gwamnatin kirki itace wacce ta ke tabbatar da biyan bukatar jama’arta. Abun takaici ne yadda tsoffin kuraye hadamammu suka dabaibaye gwamantin jihar Bauchi, wadanda basu da wani buri sai tara dukiya ta kowacce hanya.

Idan zamu iya tunawa kafin gwamnatin ta cika shekara daya aka karagar mulki wadanda suka ba da gudumawar dukiyarsu wajen kawo gwamnatin suka fara murabus daga gwamnatin bisa radin kansu a daidai lokacin da aka fi bukatar gudumawar dukiyoyi da ilimi da kuma dabarunsu wajen magance matsalolin jama’a. Wannan gwamnati tana rashin matasa masu ilimi da sanin ya kamata wadanda za a yi amfani da su wajen kai jihar tudun na tsira.

Fassarawa: Muhammad Sani Mu’azu.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *