March 11, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Hatsarin mota ya hallaka fasinjoji 12 a jihar Edo bayan direban ɗaya daga cikin motocin da suka yi karo ya yi bacci.

Wani mummunan hatsari ya afku a safiyar Asabar a kan babbar hanyar Benin zuwa Auchi, in da fasinjoji 12 suka kone kurmus a wata haɗuwa da ta faru tsakanin mota kirar Toyota Hiace da wata babbar mota.

Punch ta rawaito, Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen jahar Edo Cyril Mathew wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce hatsarin ya faru da misalin karfe 5 na safe a kauyen Igueoviobo, kusa da wurin binciken sojoji a kan titin.

A cewar sa, motar Toyota Hiace da ta bar Zuba a Babban Birnin Tarayya ta na kan hanyar ta zuwa Benin, lokacin da ta yi karo da babbar mota da ke tafiya zuwa Auchi.

Dukkan fasinjojin da ke cikin motar sun mutu a hatsarin.

“Hatsarin ka iya faruwa ne sakamakon gajiya, in da ake zaton direban motar fasinjan ya yi barci yayin tuƙi, wanda ya haddasa haɗuwar,” in ji shi.

Sakamakon haɗuwar, motar fasinjan ta kama da wuta gaba ɗaya, wanda hakan ya hana ceto rayukkan mutanen da ke ciki.

Mathew ya bayyana cewa jami’an hukumar FRSC sun gano sunayen mamatan ta hanyar takardar rajistar fasinjojin da ke cikin motar, kuma an riga an sanar da iyalan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *