Akalla mutum shida sun rasa rayukkan su bayan wata babbar mota dauke da kayan abinci ta kwace daga hanya, kuma ta kife a yankin Ugwu-Onyeama kan tagwayen titin Enugu zuwa Onitsha a Jihar Enugu.
Kwamandan hukumar Kiyaye Hadurra ta ƙasa reshen Jihar Enugu Franklin Agbakoba, ya tabbatar da afkuwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a Enugu.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hadarin ya faru ne kimanin wata guda bayan da mutane 23 suka rasa rayukan su a gobarar wata motar dakon man fetur a wannan yankin na Ugwu-Onyeama.
Agbakoba ya bayyana cewa wannan mummunan hadari ya faru da misalin karfe 8 na safe a ranar Alhamis.
Da samun kiran gaggawa jami’an hukumar kiyaye hadurra suka garzaya wurin da hadarin ya faru, inda suka ceto mutane uku da aka kai Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Jihar Enugu domin samun kulawa.
Ya bayyana cewa babbar motar wadda ke dauke da kayan lambu da ‘yan kasuwa kadan, tana gudu sosai kafin ta kwace daga hanya kuma ta kife.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja