Hukumar Kididdiga ta Ƙasa NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya sauka zuwa kaso 22.97% a watan Mayu 2025, idan aka kwatanta da 23.71% da aka samu a watan Afrilu na wannan shekara.
A cewar bayanan da hukumar ta fitar a ranar Litinin, farashin abinci a watan Mayu ya tashi da 2.19% idan aka duba a matakin wata zuwa wata wanda ya haura da 0.12% idan aka kwatanta da 2.06% da aka samu a watan Afrilu.
Hukumar ta danganta hauhawar da raguwar farashin wasu kayayyakin abinci kamar doya, rogo, masara, fulawa da dankalin turawa.
Amma idan aka duba a matakin shekara zuwa shekara, farashin abinci ya sauka zuwa 21.14% a watan Mayu 2025, wanda ya ragu da 19.52% idan aka kwatanta da 40.66% na Mayu 2024.
NBS ta ce wannan sauyi mai yawa ya samo asali ne daga sabunta shekara gwaji zuwa sabuwar shekara.
Adadin hauhawar farashi na gaba ɗaya a matakin shekara-shekara ya ragu da 10.98%, daga 33.95% a Mayu 2024 zuwa 22.97% a Mayu 2025.
A matakin wata zuwa wata an samu raguwar hauhawar farashi daga 1.86% a Afrilu zuwa 1.53% a Mayu 2025.
Adadin hauhawar farashi na birane a Mayu 2025 ya tsaya a 23.14%, yayin da a ƙauyuka aka samu 22.70% — dukansu sun ragu idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
A matsakaitan kididdiga na shekara hauhawar farashi na birane ya tsaya a 29.30%, yayin da na kauyuka ke 25.56%