April 4, 2025

Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta ficewar Nijar daga rundunar hadin gwiwa ta MNJTF.

Hedkwatar Tsaro ta karyata rahotannin da ke cewa Jamhuriyar Nijar ta janye daga Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa, tana mai cewa irin wannan matakin zai haifar da mummunan tasiri ga tsaron kasashen biyu.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa, yayin da yake jawabi a taron manema labarai a Abuja a ranar Alhamis, Daraktan Ayyukan Watsa Labarai na Tsaro Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana cewa MNJTF na ci gaba da kasancewa wani muhimmin tsarin hadin gwiwar tsaro na yankin, yana jaddada cewa dole ne a yi kokari don hana kowace kasa janyewa.

Manjo Janar Kangye ya nanata cewa, irin wannan janyewar ba zai zama mai amfani ga Najeriya ko Jamhuriyar Nijar ba.

Ya ce “Idan ka ji ‘an ce,’ hakan na nufin bayanin ba shi da inganci. Ina ganin wannan batu ya kasance abin tattaunawa tsawon watanni da suka gabata, musamman lokacin da wasu mambobin ECOWAS suka yanke shawarar kafa kawance tare da kokarin ficewa daga ECOWAS.

“Amma kamar yadda kuka sani, Rundunar Hadin Gwiwa ta Kasa da Kasa an kafa ta ne a Hukumar Tafkin Chadi don magance matsalolin tsaro na bai daya”.

“Najeriya na kokari matuka wajen tabbatar da dorewar wannan runduna. Duk da haka idan wani wata kasa mamba ta yanke shawarar ficewa, hakan zai haifar da manyan matsaloli. Hadin gwiwar da muke da ita zai iya raguwa” inji shi.

Kangye ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa, hukumomin tsaro na ci gaba da kokarin cafke fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji.

Ya karyata raɗe-raɗin da ke cewa sojoji sun rage yawan farmakin su kan makiyaya, da ‘yan ta’adda da masu satar shanu da sauran su da dama.

Dangane da jin dadin dakarun da suka jikkata, Kangye ya musanta zargin cewa an yi ko-oho da sojojin da suka samu raunukka a filin daga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *