Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Shalkwatar tsaron Najeriya ta musanta zargin da ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta Amnesty Internationa, ta yi cewa mutum 10,000 ne suka mutu a hannun sojojin, tun bayan ɓarkewa rikicin Boko Haram a Arewa maso Gabashin Najeriya.
Daraktan ƙungiyar Amnesty a Najeriya, Mallam Isa Sanusi ne bayyana zargin sojojin da hannu a mutuwar mutanen da sauran nau’ikan cin zarafi, a wani jawabi da ya yi a tarin manema labarai a birnin Maiduguri.
Isa Sanusi a ce tuni ƙungiyarsu ta shigar da ƙara gaban kotun hukunta manyan laifuka ta ICC da ke birnin Hague kan zarge-zarge take haƙƙin ɗan’adam da take yi wa sojojin a yankin Arewa maso Gabashin ƙasar.
Sojan saman Nijeriya sun yi wa Ƴan Boko Haram fata-fata a Borno.
An yi arangama tsakanin makiyaya da manoma a jihar Gombe.
Sojojin Najeriya sun yi raga-raga da sansanonin ƴan bindiga a jihar Taraba.
To sai dai yayin da take mayar da martani shalkwatar tsaron ƙasar, cikin wata sanarwa da kakakinta, Manjo Janar Edward Buba ya fitar ranar Juma’a ya bayyana zarge-zargen da masu tayar da hankali, kuma marasa tushe, kuma marasa hujja’.
“Duk da cewa yaƙin da sojoji ke yi a yankin Arewa maso gabashin Najeriya mai sarƙaƙiya ne cike da ƙalubale, muna bin ƙa’idojin da suka kamata. A duk lokacin da muka kama waɗanda ake zargi bayan ɗaukar bayanansu, mukan miƙa su hannun hukumomin da ya kamata domin a sake su ko a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Manjo Janar Edward Buba.
Sanarwar ta kuma ce shalkwatar tsaron ta gayyaci ƙungiyar ta Amesty zuwa ofishinta domin tabbatar da zarge-zargen.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.
-
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.