October 16, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Hezbollah Ta Fatattaki Sojojin Isra’ila A Ƙoƙarinsu Na Kutsawa Lebanon.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wasu rahotanni na cewa, Hezbollah ta ce ta yi ma sojojin Isra’ila kwanton ɓauna da daddare da abubuwa masu fashewa yayin da suke ƙo ƙarin kutsawa cikin Lebanon a kan iyakar ƙasar da Isra’ila da ke gabashin Lebanon.

BBC ta rawaito, ƙungiyar ta kuma ce ta yi nasanar korar wasu sojojin Isra’ilar da ke ƙoƙarin shiga ƙasar ta kan iyakar Yammacin Lebanon.

Ƙungiyar Hezbollah Ta Harba Rokoki Kan Runbun Jiyar Makaman Isra’ila A Tsakar Daren Jiya.

Za Mu Ɗauki Matakin Da Ya Dace Kan Isra’ila Ta Ƙarfin Tuwo.-Khamene.

Gagarumar Zanga-zanga Ta `Barke A Isra’ila Yayin Hezbollah Ke Zafafa Hare-hare Kan `Kasar.

Isra’ila ba ta ce komai kan haka ba, sai dai ta ce an jikkata sojanta a wani gumurzu a Kudancin Lebanon a yau Laraba, an kuma jikkata wasu biyu a ranar Talata.

Ana ci gaba da gumurzu a yaƙin da Isra’ila ke yi da Hesbollah a yankin Gabas Ta Tsakiya, abin da ke ƙara kawo zaman ɗar-ɗar a yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *