January 22, 2025

Hukumar EFCC ta ba wa jami’anta umarnin bincikar gwamnonin da ke kan mulki.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Wasu rahotanni a Najeriya na cewa, Hukumar Yaƙi da Rashawa ta ƙasar EFCC ta umurci jami’anta su ɗauki matakin binciken hatta gwamnonin da ke kan mulki kan aiyukan almundahana da yi wa tattalin arzikin ƙasar zagon ƙasa.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar Cibiyar Dimokuraɗiyya da Ba da Agajin Zaɓe reshen Afirka —International Institute for Democracy and Electoral Assistance a ziyarar da ta kai ofishinsa a wannan makon.

Aminiya ta rawaito, shugaban hukumar Ola Olukoyede ya ce hukuncin kotun da ya kori bukatar gwamnonin 19 da gwamnan Kogi Usman Ododo ya ke kan gaba wajen neman Kotu ta soke hukumar ya ƙara ba su ƙwarin gwiwa.

APCin Kano Na Son EFCC Ta Yi Bincike Kan Bidiyon Ɗan Bello.

Mataimakin shugaban Majalisar Dattawa ya raba Babura dubu 1 ga Ƴansandan Kano.

Atiku ya ja kunnen shugaba Tinubu kan ciyo wa Najeriya bashi.

Olukoyede ya ce jami’an EFCC suna da dama su tattara bayanan tuhumar gwamnonin da ke kan kujerar mulki amma ba za a dau wani mataki a kansu ba na gurfanarwa a gaban kotu ko makamncin haka har sai bayan wa’adin gwamnonin ya ƙare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *