Daga Suleman Ibrahim Modibbo.
Wani rahoto da Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta fitar wanda wanda ya shafi ayyukan ta a watan Nuwamba na 2024 ya ce, hukumar ta samu nasarar tseratar da mutum 4 daga iftila’in gobara in da mutum 3 suka mutu.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya aike wa da Martaba FM Online, ya ce, hukumar ta karɓi kiraye-kirayen neman agajin gaggawa 29 a jihar, wanda suka haɗa da kiran kashe gobara da kiran neman agajin gaggawa da kuma kiran ƙarya.
“Mun samu kira 43, sai na neman agajin gaggawa guda 5, mun kuma karɓi kiran ƙarya 6”, in ji hukumar.
Gobara Ta Tashi A Ofishin Ƴansanda A Jihar Kano.
Malaman Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Gwamnatin Kano sun tsunduma Yajin Aiki.
Kotu ta wanke wata tsohuwa daga zargin kisan kai da a jihar Kano.
Hukumar ta kuma ce, an rasa dukiya sanadiyar tashin gobara da ta kai ta naira 132,450,000, sun kuma kuɓutar da dukiyar da ta kai naira 310,600,000 daga tashin gobara.
Ta yi kira ga al’ummar jihar Kano da su kula da yadda su ke amfani da wuta, tare da tabbatar da sun kashe ta a duk lokacin da suka gama amfani da ita, “su tabbatar sun kashe ta yadda ya kamata, musamman lokacin sanyi”‘, a cewar hukumar.
A ƙarshe shugaban hukumar Alhaji Hassan Ahmad Muhammad, ya ja hankalin masu tafiye-tafiye da su yi tuƙi cikin nutsuwa musamman a lokacin bukukuwan Kirsimeti.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.