April 1, 2025

Hukumar Kwastam reshen Apapa ta jihar Legas ta samar da kudaden shiga na Naira biliyan 18.9 a rana guda.

Hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya reshen Apapa, ta bayyana cewa ta samar da kudaden shiga na Naira biliyan 18.9 a rana guda daga ranar Juma’a 14 ga watan Maris.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar Tunde Ayagbalo, ya bayyana cewa wannan shi ne mafi girman kudaden shiga da aka taba samu a tarihin ofishin kwastan na Apapa.

Ya ce sabbin alkalumman kudaden da ake samu ya zarce na baya, wanda ya kasance Naira biliyan 18.2 a watan Oktoba na shekarar 2024.

Kwanturolan hukumar mai kula da yankin Babatunde Olomu, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin farkon wasu manyan nasarori da za a cimma a shekarar 2025.

Ya tabbatar da cewa hukumar ba za ta sassauta ba, wajen yaki da safarar kayayyaki ta barauniyar hanya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *