April 1, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Karɓar Ƙorafe-ƙorafe ta jihar ta tsare shugaban ƙaramar Ƙiru.

Hukumar karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta kama Shugaban Karamar Hukumar mulkin Kiru Alhaji Abdullahi Mohammed, a ranar Jumma’a bisa zargin sayar da fili na fiye da naira miliyan darai, da aka tanada domin yin filin wasa na Kafin Maiyaki.

Jaridar internet ta Solacebase ta rawaito mai magana da yawun hukumar Malam Kabir Abba Kabir, ya shaida wa mata cewa, an tsare shugaban ƙaramar hukumar kuma ana masa tambayoyi.

Ya bayyana cewa binciken hukumar ya gano cewa an saka kuɗaɗen ne kai tsaye zuwa asusun bankin Mohammed.

Kabir ya kuma bayyana cewa wani kamfani mai suna Mahasum da wasu mutane ne suka sayi filayen da aka ware domin filin wasar.

Ya bayyana cewa asusun bankin Mohammed ya karɓi fiye da naira miliyan 240 daga ranar 1 ga watan Nuwamba, 2024, lokacin da aka rantsar da shi, zuwa 27 ga watan Fabrairu, kuma an riga an kwato su.

Kabir ya ƙara da cewa Mohammed ya na ba da haɗin kai wajen binciken da hukumar ke yi, wanda ke da nufin gano gaskiyar cinikin filayen, da kuma gurfanar da masu hannu a wannan badaƙala a gaban shari’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *