Shugabancin jam’iyyar PDP na ƙasa ya bayyana hukuncin da Kotun sauraren ƙararrakin Zaɓen Gwamnan jihar Edo ta yanke, a matsayin babban tauye adalci da kuma cin amanar da ‘yan Najeriya, musamman mutanen jihar Edo, suka nuna wa kotun.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa Hon. Debo Ologunagba, a cikin wata sanarwa ya dage cewa la’akari da yawan hujjojin da aka gabatar kuma kotun ta amince da su, ya bayyana ƙarara cewa dan takarar su Dr. Asue Ighodalo ne ya ci zaben gwamna na jihar Edo, da aka gudanar a ranar 21 ga Satumba 2024, kasancewar sa wanda ya fi kowa samun sahihan kuri’un da aka kada.
Reshen jam’iyyar a jihar da kuma ɗan takarar ta Dr. Asue Ighodalo, suma sun yi watsi da hukuncin kotun, inda suka kira hukuncin a matsayin “babban kuskure da tauye adalci.”
Shugaban jam’iyyar a jihar Edo Tony Aziegbemi, a cikin wata sanarwa ya ce duk da girmamawa da jam’iyyar ke da ita ga kotu, ba ta amince da hukuncin ba, kuma za ta daukaka kara zuwa Kotun daukaka ƙara.
Ya ce “Muna da tabbaci cewa dan takarar mu Asue Ighodalo ne mutumin da mafi yawan masu kaɗa kuri’a suka zaba a wannan zabe, kuma mun gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu.
“Saboda haka, muna kira ga mambobin mu da su tashi daga wannan jinkirin da muka fuskanta na dan lokaci, domin yanzu lokaci ne da za mu ɗaukaka ƙara zuwa Kotun ɗaukaka Kara.” inji shi.
Ighodalo a nasa bangaren ya bayyana rashin amincewar sa da hukuncin, amma ya jaddada biyayyar sa ga doka da oda tare da kudurin daukaka kara.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Babu wani gurbi a gidan gwamnatin Delta cewar Dennis Guwor ga ƴan takarar gwamnan jihar.