Daga Suleman Inbrahim Modibbo
Ɗan takarar majalisar jiha a karamar hukumar Dala da ke jihar Kano a jam`iyyar PRP Ali Rabi`u Ali Dadi, ya shaya alwashin kawo canji a jihar Kano kan shugabanci, inda yace yana daga cikin ayyukan da zai mayar da hankali, fahimtar da mutane su gane yadda ake shugabanci.
Dadi ya bayyana hakanne cikin wani shirin kai tsaye da Martaba FM ya haska a shfinsa na facebook a makwannin baya wanda Suleman Ibrahim Modibbo ya jagoranta.
”In Allah ya tabbatar dani na zama `dan majalisa zan samar da shiri na musamman da za a rika wayarwa da mutane kai su gane yadda ake shugabanci, da kuma yadda idan kuka tura shugaba bai muku dai dai ba yadda zaku dawo dashi,” in ji Dadi.
”Cikin shirin Ali Rabi`u Ali, ya bayyana manufofinsa da ya ke son cimma kan irin wakincin da yake fatan yi da zarar ya yi nasarar zama dan majalisar jiha, a babban zaben kasar nan na shekarar 2023 da ke tafe, mun kuma tabo batutuwa masu mahimmanci a siyasar jihar Kano.
Zaku iya kallon cikakkiyar hirar da ke kasa.
https://www.facebook.com/martabafm/videos/842817633440325/
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamna Bala ya sha alwashin inganta tsaro, yaƙi da talauci, yayi yaƙin neman zaɓe a Itas
-
Bauchi: Ku Kaɗa Ƙuri’un Ku Wa Jam’iyyar PDP, Za Mu Cigaba Da Haɗa Kan Al’uma, Cewar Gwamna Bala yayin ƙaddamar da kampe
-
Ƴan siyasa ku guji amfani da mimbarin Wa’azi domin biyan bukatar ku – Abdulkarim Tilde
-
Kungiyar Matasa masu hankoron ganin Gwamna Bala ya dawo a 2023 ta gudanar da babban taron shugabannin ta a jihar Bauchi
-
Bauchi: Ɗan Takarar Majalisa A PDP Ya Yi Umarnin Al’ummar Alƙaleri Da Kirfi Su Zaɓi APC.