Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
"Ina kira ga Tinubu ya dakatar da duk abin da ya ke yi a Faransa, ya dawo gida da gaggawa domin warware matsalolin rashin tsaro"-Peter Obi - Martaba FM "Ina kira ga Tinubu ya dakatar da duk abin da ya ke yi a Faransa, ya dawo gida da gaggawa domin warware matsalolin rashin tsaro"-Peter Obi - Martaba FM

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023 Peter Obi, ya bukaci Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta dawowa gida domin fuskantar karuwar matsalar tsaro.

Obi ya bayyana hakan ne a shafin sa na X, yayin da hare-haren ‘yan bindiga da ta’addanci ke karuwa a jihohin Filato, Zamfara, Borno da wasu sassan kasar nan.

Shugaba Tinubu ya tafi kasar Faransa a ranar 2 ga watan Afrilu domin “ziyara ta aiki” wacce za ta dauki tsawon makwanni biyu.

Daniel Bwala Mai ba Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin sadarwa, ya ce tafiyar na da nufin duba ci gaban sauye-sauyen da ake yi, da kuma tsara shirye-shiryen gudanarwa yayin da ake shirin cika shekaru biyu a mulki.

A cikin sakon sa na ranar Laraba, Obi ya ce ya ga ya zama wajibi ne ya jawo hankalin shugaban kasar da ke ja da baya zuwa ga matsalolin tsaro da ke addabar gida, yana mai cewa ya kamata ya dakatar da ja da baya da yake yi a kasar waje, ya dawo gida domin fuskantar halin da ake ciki na tsaro a fadin kasar.

A cewar sa, kiran da yake yi ya zama dole ne sakamakon karuwar laifukka da aikata miyagun ayukka a fadin Najeriya, tare da rashin tabbas na shugabanci.

“Cikin makwanni biyu da ka yi a waje, sama da ‘yan Najeriya 150 ne suka rasa rayukan su sakamakon rashin tsaro a fadin kasar nan musamman a jihohin Filato da Zamfara. Fashewar bututun mai da ke yawan faruwa a yankin Neja Delta na kara nuna cewa kasa na cikin mawuyacin hali”. Inji Obi.

Ya kara da cewa “A Arewa maso Gabas shugabannin jihar Borno na kokawa da dawowar ‘yan ta’adda, inda dakarun tsaro da fararen hula ke rasa rayukan su babu gaira babu dalili. A Kudu maso Gabas lamarin ya yi kamanceceniya; kashe-kashe da sace-sace sun zama ruwan dare.

“A tsakiyar wannan rikici, Shugaban kamfanin da ake kira Najeriya yana can nesa a kasar Faransa, ya na ja da baya daga hedkwatar kamfanin,” in ji Obi.

Ya ce “Don haka ina kira ga Shugaban kasa da ya dakatar da duk abin da yake yi a Faransa, ya dawo gida da gaggawa domin warware wadannan matsalolin da ke damun al’umma.”

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *