Wani taron jama’a da suka taru don kallon manyan motoci biyu masu sulke dake shiga cikin sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin, suna farfasa titin don buɗe hanya ga tankoki uku na Isra’ila.
“Wannan shi ne karo na farko da na taɓa ganin tanka da idona,” wani matashi furta hakan, yayin da muryar sa ke cike da mamaki da rashin yarda.
Isra’ila ta aike da tankoki a gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, tana kai hari sansanonin ‘yan gudun hijira.
Ya ce a gaban sa, manyan motocin ke ci gaba da ruguza titi suna matsawa gaba, suna ƙara lalata hanyar da ke ƙarƙashin su. Sansanin ‘yan gudun hijira wanda ya kusan zama wayam bayan makonni da dama na hare-haren soji, yana shirin fuskantar wata sabuwar mamaya, kamar yadda Aljazeera ta rawaito.
An haifi Ahmed a Jenin a shekarar 2003, a lokacin da Intifada ta biyu ke ƙara kamari. Ya taɓa ganin mamayewar sojoji a baya, amma tun daga 2002 lokacin da tashin hankalin ya fara, ba a sake ganin tankokin Isra’ila a titunan Jenin ba. Yanzu kuma, da alama Isra’ilawa na shirin zama na ɗan lokaci.