January 22, 2025

Isra’ila Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Gaza.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya sake jaddada matsayarsa kan cewa ƙasarsa ba za ta tsagaita wuta na dindindin ba, kuma dakarun ƙasar za su ci gaba da fafatawa “har ƙarshe.”

Kamar yadda BBC ke ruwaitowa, masu shiga tsakani na ƙasashen Masar da Qatar na ci gaba da ƙoƙarin ganin an tsawaita tsagauta wuta.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar, Netanyahu ya ce “Tun daga farkon wannan yaƙi na bayyana ƙudurori uku: kawar da Hamas, dawo da dukkanin mutanenmu da ake yin garkuwa da su tare kuma da tabbatar da cewa Gaza bai sake zamewa barazana ga Isra’ila ba. Har yanzu waɗannan ƙudurori na nan daram.”

Ya ce sakin gomman mutanen da ake garkuwa da su “babban ci gaba ne.”

“To amma a kwanakin nan na ji wasu na tambayar: Bayan kammala wannan mataki na dawo da waɗanda ake garkuwa da su, ko Isra’ila za ta ci gaba da yaƙin? Amsar ita ce e.”

“Babu abin da zai hana mu komawa yaƙi har sai mun kai ƙarshe, wannan ce manufata, kuma majalisar sojin na goyon bayan hakan, gwamnati tana goyon bayan haka.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *