Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Isra’ila ta nemi tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 42. - Martaba FM Isra’ila ta nemi tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 42. - Martaba FM

Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya gudanar da shawarwari tare da manyan jami’an tsaro da ministocin sa a ranar Juma’a, bayan dawowar wata tawagar Isra’ila daga Alƙahira ba tare da cimma yarjejeniya kan tsawaita zaman dakatar da bude wuta a Gaza ba, a cewar wasu jami’an Isra’ila biyu.

Wani jami’in Hamas ya tabbatar da cewa Isra’ila ta nemi tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon kwanaki 42 a matsayin matakin farko na yarjejeniyar har zuwa karshen watan azumin Ramadan, wanda zai fara a karshen mako. Sai dai ya ce Hamas tana son a shiga matakin na biyu na tattaunawar, wanda zai buɗe hanyoyin kawo ƙarshen yakin gaba ɗaya.

Masu shiga tsakani daga Masar da Qatar sun nemi karin lokaci a cikin ‘yan kwanakin nan, don kokarin warware matsalar game da tsagaita wutar, wacce za ta ƙare a ranar Asabar, kamar yadda jami’an suka bayyana.

Yarjejeniyar da aka cimma a watan da ya gabata ta kawo karshen wata 15 na fada, in da aka musanya fursunoni, Isra’ila ta saki kusan Falisdinu 2,000, yayin da aka saki ‘yan Isra’ila biyar daga Thailand. An tsara cewa wannan yarjejeniya za ta jagoranci ƙarin tattaunawa don tabbatar da tsagaita wuta na dindindin.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *