March 11, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Isra’ila ta saki Falasɗinawa sama da 600 bayan Hamas ta miƙa mata gawarwakin mutum huɗu.

Hamas ta miƙa gawarwakin Isra’ilawa huɗu da aka tsare a Gaza ga Kungiyar Agaji ta Red Cross, a matsayin wani bangare na ƙarshe a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta.

A lokaci guda, bas ɗin farko dauke da Palasdinawa fursunoni da aka sako daga gidan yari na Ofer ya isa birnin Ramallah, da ke yankin Gabar Yamma da Isra’ila ke mamaye da shi.

Wannan musayar na zuwa ne bayan Hamas ta sanar da cimma yarjejeniya da makwatan su kan sakin fursunoni 620 na Falasdinu da ya kamata a sako daga Isra’ila a makon da ya gabata, da kuma yawan dai dai da hakan na mata da yara da aka tsare tun lokacin da yaƙi ya barke. Isra’ila ta tabbatar da yarjejeniyar ba tare da bayar da ƙarin bayani ba.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric, ya buƙaci Isra’ila da ta bar ƙarin tantuna da mafaka su shiga Gaza bayan da jarirai shida ƴan Falasdinu suka mutu sakamakon tsananin sanyi.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta tabbatar da cewa Falasinawa dubu arba’in da takwas da dari uku da arba’in da takwas sun mutu a yakin da Isra’ila ke kaiwa Gaza, yayin da wasu dari daya da goma sha daya da dari bakwai da sittin da daya suka jikkata.

Ofishin Watsa Labarai na Gwamnatin Gaza ya sabunta alkaluman adadin mace-macen zuwa akalla 61,709, ya na mai cewa dubban mutane da ke ƙarƙashin baraguzan gine-gine ana kyautata zaton sun mutu.

A bangaren Isra’ila mutane 1,139 ne aka kashe a hare-haren Hamas na ranar 7 ga watan Oktoba 2023, kuma fiye da 200 aka kama a matsayin fursunoni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *