Labarai
Trending

Iyalan Sarkin Kano Ado Sun Ƙaryata Alaƙa Da Zainab Wadda Take Iƙrarin Ita Ɗiyar Sarkin ce.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.

Iyalan marigayi mai martaba Sarkin Alhaji Ado Bayero, sun nesanta kansu daga duk wata dangata da wata mata da ake cewa matar marigayi Sarki Kano na 13 ce a jihar Edo.

Cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Asabar mai ɗauke da sa hannun Aminu D.Ahmad, tsohon babban jami’in tsaron Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, ta ce labarin ko kaɗan ba gaskiya ba ne, wani shiri ne na ɓata sunan marigayin.

A ranar Juma’a ne kafofin yaɗa labaran intanet a Najeriya suka rawaito wata mata wadda ta ce sunanta Zainab Ado Bayero, wato ɗiya ga Sarkin ta na neman taimakon ɗaukin kuɗin siyen gida na naira miliyan 150 daga shugaban ƙasar Najeriya Bola Tinubu da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ta na mai cewa suna cikin wani hali na ƙunci tun bayan rasuwar Sarkin.

Ƴaƴan Sarkin sun ce, ko kaɗan labarin ba gaskiya bane, hasali ma sarkin bai taɓa auren wata mata a jihar Edo ba, ballanata ma su haihu tare.

“Waɗannan mutane suna ƙoƙarin ɓata sunan marigayi Sarki ne ta hanyar ƙirƙiro labaran da ke nuni da cewa ya auri wata mata daga jihar Edo”, in ji sanarwar.

“Mai martaba, marigayi Ado Bayero, bai auri wata mace daga jihar Edo ba a lokacin rayuwarsa”.

Sun kuma yi zargin cewa, Zainab suna bin irin wannan hanyar ce domin yaudarar mutane don su danfare su kuɗaɗe “bugu da ƙari, an ba da rahoton cewa waɗannan miyagun suna yin amfani da wannan labari na ƙarya ne don yaudara da karɓar kuɗi daga wasu mutane marasa tunani.”

Aminu D.Ahmad ya ce, iyalan Bayero da Majalisar Masarautar Kano sun duƙufa wajen ganin an kiyaye kyawawan abubuwan da Mai Martaba ya yi, muna kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan jita-jita da ba su da tushe balle makama, kada su faɗa cikin waɗannan bata-gari.

Marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, ya rike sarautar Kano ne tun daga shekarar 1963 har zuwa rasuwarsa a shekarar 2014.

Ko a watan Yunin da ya gabata sai da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya taimaka mata da kuɗin da suka biya hayar gidan da suke zaune a Legas bayan an yi shirin tashin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button