Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
“Jama’a suna komawa APC ne saboda suna ganin abubuwa masu kyau"-Gwamnan Nasarawa - Martaba FM “Jama’a suna komawa APC ne saboda suna ganin abubuwa masu kyau"-Gwamnan Nasarawa - Martaba FM

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba ta da wani shiri na mayar da Najeriya mai tsarin jam’iyya ɗaya duk da yawaitar sauya sheƙa daga ‘yan adawa zuwa jam’iyyar mai mulki.

Da ya ke zantawa da manema labarai a ranar Talata bayan wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban ƙasa, gwamna Sule ya ce, “Ba ma son Najeriya ta koma ƙasa mai jam’iyya jam’iyyar ɗaya. Abin da muke so shi ne mu mamaye mafi yawan kuri’u. Idan muka iya samun kaso 90 cikin ɗari, wannan ya na da kyau. Wasu jam’iyyun su rike sauran kashi 10. Ba na yi da barkwanci, da gaske nake.”

Gwamnan ya ce APC na girmama tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama, in da ya ce ko a ƙasashen waje irin su Amurka, ana da jam’iyyun adawa da dama kamar su Republican da Democrat.

Dangane da sauya shekar da ‘yan siyasa ke yi zuwa APC, Gwamna Sule ya danganta hakan da sabbin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Tinubu ke aiwatarwa, ciki har da cire tallafin mai, da daidaita farashin canjin kuɗi da kuma gyare-gyaren ɓangaren wutar lantarki.

“Duk wani sauyi ya na zuwa da kalubale, amma fa’idodinsa sun fi yawa,” in ji shi. “Jama’a suna komawa APC ne saboda suna ganin abubuwa masu kyau.”

A wani bangare na tattaunawar, Gwamna Sule ya ce Nasarawa na ci gaba da karɓar manyan jarin masana’antu, yana mai bayyana cewa jihar yanzu ita ce ke da mafi yawan mini-grid na wutar lantarki a ƙasar, kuma tana samun ci gaba a fannoni kamar noma da ma’adanai.

Ya bayyana cewa jihar na shirin ƙaddamar da wani sabon kamfanin sarrafa ma’adanan lithium wanda ya ninka girman wanda aka ƙaddamar a bara sau uku. Haka kuma, ya ce wasu masana’antun sarrafa lithium da tantalite za su fara aiki kafin ƙarshen shekarar nan.

“Nasarawa na jawo masu zuba jari saboda zaman lafiya da kuma yanayin da ke sauƙaƙa kasuwanci,” in ji gwamnan.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *