Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Hukumar JAMB mai shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya, ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da dalibai suka zana a bana.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Dr Fabian Benjamin ya fitar ranar Lahadi a Abuja, babban birnin tarayya kamar yanda Jaridar Punch ta ruwaito.
Hukumar shigar da manyan makarantu ta hadin gwiwa ta kammala shirye-shiryen fitar da sakamakon jarrabawar kammala manyan makarantu na shekarar 2024.
Magatakardar Hukuma ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, na shirin ganawa da manema labarai a Abuja a yau Litinin dan fitar da sakamakon da kuma abubuwan da suka danganci hakan, kamar yadda sanarwa da aka raba wa manema labarai a babban birnin tarayya.
Duk da haka, akwai alamun cewa sakamakon da za a fitar a yau Litinin ya kasance na dalilai da suka zana UTME a cikin ‘yan kwanaki na farko, yayin da wasu za a fitar da su bayan an kammala.
Tun da farko dai hukumar ta fayyace cewa an yanke shawarar jinkirta fitar da sakamakon na ‘yan kwanaki ne domin a ba da isasshen lokaci domin yin nazari sosai.
Wannan matakin, a cewar hukumar jarrabawar, an dauki wannan mataki ne domin tabbatar da gaskiya da ingancin sakamakon da aka samu, tare da tabbatar da cewa babu shakka ko rashin tabbas, musamman dangane da batutuwan da suka shafi kwaikwaya, gaurayawan na’urorin zamani, da sauran nau’ukan munanan ayyuka.
A cikin makon da ya gabata, sama da ’
dalibai miliyan 1.9 ne suka yi rajista don jarrabawar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.