Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Tawagar haɗin gwiwa ta ’yan sanda, sojoji da ’yan sa-kai, sun ceto manoma 36 da ’yan bindiga su ka sace a ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu a Jihar Kebbi.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, ya bayyana cewa ’yan bindiga sun tare manoman da ke dawowa daga gonakinsu, inda suka yi awon gaba da su.
Rundunar haɗin gwiwar ta yi gaggawar kai ɗauki, inda suka yi nasarar fatattakar ’yan bindigar zuwa cikin daji, yayin da wasu daga cikinsu suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Babban hafsan Sojin ƙasa ya sha alwashin kawo ƙarshen Ƴan ta’addan Lakurawa cikin kankanin lokaci.
Sojojin Najeriya sun yi raga-raga da sansanonin ƴan bindiga a jihar Taraba.
Sojan saman Nijeriya sun yi wa Ƴan Boko Haram fata-fata a Borno.
Sanarwar ta tabbatar da cewa an ceto dukkanin manoma 36 ba tare da sun samu rauni ba, kuma an miƙa su ga iyalansu.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Bello M. Sani, ya yi kira ga dukkanin hukumomin tsaro a yankin da su ƙara haɗa kai don yaƙi da ’yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.