Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Oyo ta kama dalibbai 59 na Makarantar Fasaha ta Gwamnati dake Orita-Aperin, bisa laifin kai hari da lalata dukiyoyi a Makarantar Christ Apostolic Grammar Ibadan.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Johnson Adenola ya tabbatar da hakan a ranar Litinin a Ibadan, yayin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Hedikwatar Rundunar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, an shirya taron ne domin hana sake afkuwar rikice-rikicen kungiyoyi a makarantu a jihar Oyo.
A cewar Adenola dalibban Makarantar Fasaha ta Gwamnati Ibadan, sun tayar da tarzoma a ranar Alhamis inda suka afkawa harabar makarantar Grammar.
“Dukiyoyin da aka lalata sun hada da motoci, dakin gwaje-gwaje na makaranta, sannan wasu malammai sun samu raunukka a lokacin harin,” in ji Kwamishinan ‘Yan Sanda.
Ya kara da cewa an sami dalibbai 17 daga cikin 59 da aka kama da laifi, yayin da aka saki sauran ba tare da tuhume-tuhume ba.
Ya ce “Lokacin da na yi hira da su a ranar Assabar, na yi mamakin tarzomar da suka yi. Yawan lalacewar tarbiyya a makarantu a fadin jihar Oyo yana da matukar tayar da hankali.
“An lura da cewa dalibbai da dama suna haddasa rikice-rikice, musamman bayan kammala jarabawar zangon karatu ko karshen shekarar makaranta.
“Wannan dabi’a ba za ta ci gaba da kasancewa ba, dole ne a kawo karshenta nan take,” in ji Kwamishinan.
Ya bayyana cewa tattaunawar da aka yi a taron ta kasance mai amfani, tare da kokarin dakile rikicin kungiyoyin makarantu kafin ya yi kamari.
Ya bukaci iyaye da masu kula da yara su sa ido sosai a kan ‘ya’yan su, yana mai cewa ba wai bayar da kudi kawai ba ne ke tabbatar da tarbiyyar yara yadda ya kamata ba.
Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar Oyo Farfesa Saliu Adelabu, ya yaba wa ‘yan sanda bisa irin yadda suka dakile lamarin cikin kwarewa.
NAN ya ruwaito cewa wadanda suka halarci taron sun hada da shugabannin makarantu, Shugaban Hukumar SUBEB ta jihar Oyo Dakta Nurein Adeniran, da kuma iyayen dalibban da abin ya shafa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja
-
Fasinjojin wata mota huɗu sun riga mu gidan gaskiya wasu kuma sun jikkata a jihar Borno.